7 Janairu 2020 - 05:59
Yau Za’a Binne Gawar Shahid Suleimani A Mahifarsa Kerman

A Iran, yau ne ake sa ran za’a binne gawar shahid Qasim Sulaimini, a mahaifarsa dake birnin Kerman.

(ABNA24.com) A Iran, yau ne ake sa ran za’a binne gawar shahid Qasim Sulaimini, a mahaifarsa dake birnin Kerman.

A jiya Litini ne aka yi wa mirigayin tare da wasu shahidan sallar janaza a nan birnin Tehran tare da halartar manyan jami’an kasar a sahun gaba jagoran juyin juya halin musulinci na kasar Ayatollah Sayid Ali Khamenei, wanda ya jagoranci sallar janazar.

Taron janazar na jiya an bayyana shi da mafi girma a tarihi, wanda kuma ya nuna so da kaunar da jama’ar kasar daman a wasu yankin ke wa Janar Qasim Sulaimani din, da kuma tsayin dakan da ya yi wajen kare manufofin kasar da kuma yaki da ta’addancin kungiyar da’esh musamman a kasashen Siriya da Iraki.

Da sanyin safiyar ranar Juma’ar data gabata ce, Janar Qasim Sulaimani, babban kwamandan rundinar Quds ta dakarun kare juyin juya halin muslinci ta Iran ya yi shahada tare wasu shahidai dake tare da shi irinsu Abu Mehdi Muhandis a wani harin saman Amurka a kusa da filin jirgin saman Bagadaza na kasar Iraki.

Iran dai ta sha alwashin daukan mummunan fansa kan kisan, a lokaci da kuma inda ya dace, a daidai lokacin da kasashen duniya ke ta kiraye kirayen kai zuciya nesa.



/129